Daga Laraba

著者: Muslim Muhammad Yusuf Ummu Salmah Ibrahim
  • サマリー

  • Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.

    © 2024 Daga Laraba
    続きを読む 一部表示

あらすじ・解説

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.

© 2024 Daga Laraba
エピソード
  • Matsayin Gwamnonin Arewa Kan Kudurin Haraji – Kishin Kasa Ko Son Zuciya?
    2024/10/30

    Taron da Kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) ta yi a Kaduna ya bar baya da kuria’a.
    Daya daga cikin shawarwarin da gwamnonin suka yanke ita ce ta kin amincewa da wani Kuduri da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya kai Majalisar Dokoki ta Kasa.

    Shin kishin Arewa ne ya sa gwamnonin suka yi Allah-wadai da Kudurin ko kuma son zuciya?

    Wannan ce muhawarar da ta biyo bayan sanarwar bayan taron na NGF, kuma shirin Daga Laraba zai lalubo amsarta.

    続きを読む 一部表示
    28 分
  • Shin Duka Ne Hanyar Ladabtar Da Yara Mafi Inganci?
    2024/10/23

    Tarbiyya kamar yadda aka san ta a al’adance tana inganta ne idan al’umma gaba daya ta hada hannu wajen ladabtar da yara.

    Duk wanda ya kai shekaru talatin zuwa sama ya san cewa a da can iyaye da sauran jama’ar gari suna iya daukar tsumagiya don ladabtar da shi idan ya kauce hanya.

    Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi duba ne kan alfanun ko illar hakan wajen ladabtar da yara.

    続きを読む 一部表示
    26 分
  • Me Ya Sa Kimar Dattawa Ta Ragu A Cikin Al’umma?
    2024/10/16

    Afrika na da dadadden tarihin girmama na gaba, musamman dattawan da ke cikin al’umma.

    Sai dai a wannan zamani akan samu matashi ya shafa wa idonsa toka ya fito bainar jama’a yana musayar zafafan kalamai da sa’o’in mahaifinsa.
    Shin me ya sa ake samun irin wannan?

    Don jin amsar wannan tambaya da ma wasu sai ku biyo mu a cikin shirin Daga Laraba na wannan makon.

    続きを読む 一部表示
    30 分

Daga Larabaに寄せられたリスナーの声

カスタマーレビュー:以下のタブを選択することで、他のサイトのレビューをご覧になれます。