エピソード

  • Shin Addu’oi Kadai Najeriya Take Bukata Don Ficewa Daga Matsaloli?
    2024/11/05

    Send us a text

    Galibin ’yan Najeriya dai sun yarda cewa Allah ne mai bayarwa, Shi ne kuma mai hanawa.

    Mai yiwuwa hakan ne kan sa a rika yin kira, musamman ga mabiya addianai mafiya rinjaye na Musulunci da Kiristanci, da su yi addu’oi don samun waraka daga matsalolin da aka fama da su.

    Sai dai kuma wasu ’yan kasa suna ganin fadar haka alama ce da take nuna cewa siukuwa ta kare saura zamiya.

    Shirin Najeriya A Yau zai yi Nazari ne kan wannan batu.

    続きを読む 一部表示
    28 分
  • Abin Da Ya Kamata A Yi Da Kananan Yara Masu Zanga-Zanga
    2024/11/04

    Send us a text

    Gurfanar da yaran nan da aka kama watanni uku da suka gabata yayin zanga-zangar ‘#EndBadGovernance’ na ci gaba da yamutsa hazo a Najeriya.

    Mutane da dama dai, musamman a Arewa, suna ta tofin Allah-tsine a kan kamen yaran, wadanda wasu suke cewa kanana ne, shekarunsu ba su kai a kama su ba ballantana a kai su gaban kotu.

    Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai tattauna ne kan tanadin doka game da kamen kananan yara, da kulle su, da kuma gurfanar da su gaban kuliya.

    続きを読む 一部表示
    28 分
  • Yadda Dawo Da Wutar Lantarki Zai Sauya Wasu Sassan Arewa
    2024/11/01

    Send us a text

    A wasu sassan Arewa, mutane sun cika da farin ciki da annashuwa bayan da wutar lantarki ta dawo a yankunansu.

    Yankin na Arewa dai ya tsinci kansa cikin rashin wutar lantarki na kusan kwanaki goma bayan da babban layin dakon wutar lantarkin ya durkushe.

    Shirin Najeriya A Yau zai duba tasirin dawowar lantrakin a yankin na Arewa.

    続きを読む 一部表示
    27 分
  • “Matsin Tattalin Arziki Ya Sa Ba Na Iya Aikina Yadda Ya Kamata”
    2024/10/31

    Send us a text

    Alamu sun nuna cewa sakamakon kuncin rayuwa da ake fama da shi a Najeriya, ingnacin aikin da ma’aikata suke yi yana raguwa.

    Aiki yana ingnatuwa ne dai da samun wasu abubuwa da suka hada da kyakkyawan yanayin wurin aiki da isasshen hutu da kwanciyar hankali da kuma biyan bukatar ma’aikaci a dukkan lokaci.

    Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai tattauna ne kan yadda matsin tattalin arziki ke shafar ayyukan ma’aikata da ma masu aikin hannu a Najeriya.

    続きを読む 一部表示
    29 分
  • Dalilan Da Ake Cin Zarafin ‘Yan Najeriya
    2024/10/29

    Send us a text

    Cin zarafi da daidaikun alumma ke fuskanta a Najeriya yayin da suke gudanar da ayyukan su na yau da kullum ba sabon abu bane, musamman la’akari da cewa mutanen biyu a mafi akasarin lokaci basu san abun da doka ta tanada game da cin zarafi ba.

    A wasu lokuta ma, cin zarafin nan na fito wa ne daga wadanda suke rike da madafun iko, inda zaka ga suna bayyana cewar ‘’zan keta maka haddi kuma babu abun da zai faru’’.

    Shirin Najeriya A Yau zai yi duba ne kan wannan batu na Cin Zarafi.

    続きを読む 一部表示
    21 分
  • Ko Wadanne Dalilai Ne Ke Sanya Wasu ‘Yan Najeriya Ajiye Ababen Hawan Su?
    2024/10/28

    Send us a text

    Tsadar man fetur a Najeriya ya tilastawa da yawa daga cikin ‘yan kasa ajiye ababen hawan su inda suka koma bin na haya don zuwa wuraren aiki, Ziyara da sauran zirga-zirgar su ta yau da kullum.

    A baya manyan biranen Najeriya su kan cika su batse da ababen hawa da kan yi zirga-zirga da kai kawo, wanda wasu suke ganin wadata da fin karfin bukatun yau da kullum ne ke sanya hakan.

    Shirin Najeriya A Yau na wannan rana yayi duba ne kan yanda wasu ‘yan Najeriya suke ajiye ababen hawan su suna komawa bin na haya....

    続きを読む 一部表示
    25 分
  • Kuncin Da Arewa Ta Shiga Sakamakon Rashin Wutan Lantarki
    2024/10/25

    Send us a text

    Fiye da mako guda ke nan wasu sassan arewacin Najeriya suna fama da rashin wutar lantarki.

    Hakan ya haddasa gagarumar matsala a rayuwar mutane da dama.

    Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai duba irin halin matsi da mazauna yankin suka shiga sakamakon daukewar wutar lantarkin.

    続きを読む 一部表示
    23 分
  • Ko Garambawul Din Da Tinubu Ya Yi Zai Kawo Wa ’Yan Najeriya Sauki?
    2024/10/24

    Send us a text

    A karon farko tun bayan rantsar da shi, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sauye-sauye ga Majalisar Ministocinsa.

    ’Yan Najeriya dai sun dade suna jiran wannan garambawul din na Shugaban Kasa; said ai abin tambaya shi ne: mene ne zai biyo bayan wannan garambawul din?

    A kan wannan batu shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari.

    続きを読む 一部表示
    27 分